23 Oktoba 2019 - 10:48
Guinea : An Daure Jagororin Masu Boren Kin Jinin Shugaba Conde

Wata kotu a birnin Conakry, na kasar Guinea, ta yanke hukuncin zama gidan yarina wata shida zuwa shekara guda, ga jagorin masu zanga zangar kin jinin tazarcen shugaban kasar Alpha Conde a zaben 2020.

(ABNA24.com) Tuni jam’iyyar adawa ta kasar (FNDC), ta yi tir da matakin kotun, tare da danganta kotun da ‘yar amshin shatan masu mulkin kasar.

Madugun kawancen jam’iyyun adawan da kuma kungiyoyin fara hular dake zanga zangar, Abdourahamane Sanoh, na daga cikin wadanda aka yanke wa irin wannan hukuncin, inda aka yanek masa hukuncin shekara guda a gidan yari.

An dai zarge da tada zaune tsaye ta hanyar kiran zanga zanga da kuma neman durkusar da tattalin arzkin kasar.

‘yan adawa a kasar dai sun bayyana cewa mutane 10 ne aka kashe yayin zanga zangar data soma a ranar 14 ga watan nan.

..........
340